'Laifinmu ne idan City ta yi ta biyar a Premier'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Manchester City za ta buga wasan karshe da Swansea a ranar Lahadi

Dan kwallon Manchester City, Bacary Sagna, ya ce laifin 'yan wasa za a gani idan har kungiyar ta kare a mataki na biyar a Premier bana.

Wasa daya City ta ci daga guda hudu da ta yi a baya a gasar Premier, ciki har da wanda ta tashi 2-2 da Arsenal.

Hakan ne ya sa kungiyar ke mataki na hudu a kan teburi da maki 65, yayin da Manchester United ke da maki 63 a matsayi na biyar.

Idan har United ta ci kwantan wasan Premier da za ta yi da West Ham da kuma wasan karshe da za ta buga da Swansea za ta koma ta hudu a teburi.

Sagna ya ce sakacin 'yan wasa ne idan har City ba ta kare a mataki na hudu ba, domin sune suka barar da damarsu.

Ya kuma kara da cewar da sun yi wasanninsu a baya da kuma sanya kwazo kamar wanda suka yi da Arsenal da ba su tsinci kansu a wannan halin ba.