Munich ta dauki Hummels da Renato

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern Munich ce ta lashe kofin Bundesliga na bana

Kungiyar Bayern Munich, ta dauki dan wasan Borussia Dortmund, Mats Hummels da Renato Sanches daga Benfica.

Hummels mai shekara 27, mai tsaron baya zai buga wa Munich tamaula tsawon shekara biyar.

Bayern ta sayi Sanchez daga Benfica kan kudi dala miliyan 27.5 wanda Manchester United ta yi zawarci.

Carlo Ancelotti ne zai maye gurbin Pep Guardiola a karshen kakar wasan bana a matsayin koci a Allianz Arena.

Pep Guardiola zai koma horar da Manchester City a badi, wanda zai maye gurbin Manuel Pellegrini a badi.

Bayern Munich ce ta dauki kofin gasar Bundesliga na Jamus na bana kuma na 26 jumulla.