Guidolin zai ci gaba da horar da Swansea

Swansea City za ta bai wa Francesco Guidolin aikin horar da kungiyar a kakar wasan badi.

Guidolin mai shekara 60, ya karbi aikin jan ragamar Swansea a cikin watan Janairu a yarjejeniyar zuwa karshen kakar bana.

Kociyan dan kasar Italiya ya ci wasanni bakwai da yin canjaras uku da rashin nasara a karawa biyar daga 15 da ya jagoranci Swansea.

A ranar Laraba ne mahukuntan Swansea za su yi taro domin tsawaita zaman Guidolin a kungiyar.

Swansea za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan karshe na gasar Premier a ranar Lahadi.