An ci kwallaye 320 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Za a fara wasannin mako na 16 a ranar Laraba

Kwallaye 320 aka ci a gasar Firimiya Nigeria, bayan da aka buga wasanni 147 a cikin mako na 15 da aka yi.

Daga cikin kwallayen da aka ci, guda 89 kungiyoyin da suka buga wasanninsu a waje ne suka ci su.

Godwin Obaje na Wikki Tourist shi ne ke kan gaba a matsayin wanda ya fi cin kwallaye a gasar, inda ya ci takwas.

'Yan wasan da suka ci bakwai a gasar kuwa sun hada da Isma'ila Gata na Niger Tornadoes da Anthony Okpotu na Lobi Stars da Ibrahim Mustapha na El-Kanemi Warriors.

Sauran sun hada da Okiki Afolabi na Sunshine Stars da kuma Chisom Egbuchulam na Rangers.

Kano Pillars ce kan gaba a matsayin wadda tafi yawan cin kwallaye a gasar, inda ta zura 24 a raga.

Enugu Rangers ce ta biyu wadda ta ci 22, sai Wikki Tourist da ta ci 20 a gasar.

Haka kuma Wikkin ce kungiyar da aka ci kwallaye bakwai a raga a matsayin wadda ba a zura mata su da yawa ba a wasannin.

Abia Warriors kwallaye takwas aka ci ta, sai Warri Wolves da guda 10 suka shiga ragarta.