West Ham ta doke Man United da ci 3-2

Hakkin mallakar hoto pa
Image caption A ranar Lahadi za a buga wasannin karshe a gasar Premier

West Ham United ta samu nasara a kan Manchester United da ci 3-2 a kwantan wasan Premier da suka buga a ranar Talata.

Sakho ne ya fara ci wa West Ham kwallo a minti na 10 da fara wasa.

Bayan da aka dawo ne daga hutun rabin lokaci Martial ya farke wa United ya kuma kara ta biyu a karawar.

Saura minti 16 a tashi wasa Antonio ya farke wa West Ham, kuma saura minti 10 a kammala wasan Reid ya ci ta uku.

West ham wadda ke neman gurbin buga gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa ta hada maki 62 tana kuma mataki na shida a teburi.

United kuwa mai neman gurbin buga gasar cin kofin zakaru ta Champions League tana mataki na biyar da maki 63.

Wannan shi ne wasan karshe da West Ham ta yi a filinta na Upton Park, inda za ta ci gaba da fafatawa a sabon filin wasa mai suna Olympic a badi.

A ranar Lahadi za a kammala gasar Premier bana, inda United za ta karbi bakuncin Bournemouth, West Ham ta ziyarci Stoke City.