Leicester za ta tsawaita zaman Ranieri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester City ta hada maki 80 a matsayi na daya a teburin Premier

Leicester City wadda ta lashe kofin Premier na bana, za ta tsawaita zaman koci Claudio Ranieri a kungiyar.

Ranieri mai shekara 64, dan kasar Italiya wanda yarjejeniyar da suka kulla za ta kare a 2018, ya jagoranci kungiyar lashe kofin Premier na bana.

Kociyan ya karbi aikin horar da Leicester City a cikin watan Yulin 2015, inda ya maye gurbin Nigel Perason.

Leicester wadda a bara ta kusa barin gasar Premier, tana mataki na daya a kan teburin bana duk da saura wasa daya a kammala gasar.

Wasanni uku kacal aka ci Leicester a kakar bana, ita kuma ta ci 23, sannan ta yi canjaras sau 11, ta kuma ci kwallaye 67 aka zura mata 35 a raga.