Sunderland za ta ci gaba da buga Premier

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Sunderland za ta ci gaba da zama a gasar Premier

Sunderland ta doke Everton da ci 3-0 a kwantan wasan Premier da suka kara a ranar Laraba.

Van Aanholt ne ya fara ci wa Sunderland kwallo, kuma bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci Kone ya ci guda biyu.

Da wannan sakamakon Sunderland tana mataki na 17 a kan teburin Premier da maki 38 duk da saura wasa daya a kammala gasar.

Hakan na nufin Norwich City da Newcastle United za su fadi daga Premier su koma buga gasar Championship a badi tare da Aston Villa.

A ranar Lahadi za a buga wasannin karshe a gasar, inda za a yi fafatawa 10 a ranar.