Caf ta sauya tsarin wasanni

Image caption A baya dai ana kungiyoyi takwas ne suke fafatawa domin neman lashe kofin na zakarun Afrika.

Hukumar kwallon kafa ta Afrika ta sauya tsarin gasar cin kofin zakarun Afrika ta Champions League da kuma ta Confederation Cup, da za a yi a 2017.

Yanzu haka dai kungiyoyin wasa 16 ne za su samu gurbin shiga kowacce daga cikin gasar, a inda za a raba su zuwa aji hudu kuma kowane aji zai kunshi kungiyoyi hudu.

A baya dai kungiyoyi takwas ne ke shiga gasar, a inda ake raba su gida biyu.

Shugaban hukumar, Issa Hayatou wanda ya sanar da hakan a lokacin taron hukumar a Mexico, ya ce sabon tsarin zai fara daga kakar wasa mai kamawa.