Tennis: An fitar da Konta daga gasar Roma

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An cinye Johanna Konta da ci 4-6 da 7-5 da 6-2

Misaki Doi ta doke Johanna Konta a wasan zagaye na uku na gasar kwallon tennis ta mata da ake yi a Rome.

Konta mai shekara 24, yar kasar Birtaniya, tasha kashi a hannun Doi da ci 4-6 7-5 6-2.

Doi wadda ke mataki na 45 a jerin wadanda suka fi iya kwallon tennis a duniya ta kai wasan zagaye na hudu a gasar kenan.

Ita ma Serena Williams ta kai wasan gaba a gasar bayan da ta ci Christina McHale da ci 7-6 (9-7) 6-1.

Williams za ta fafata da Svetlana Kuznetsova wadda ta fitar da Daria Gavrilova da ci 6-2 2-6 6-3 daga gasar.

Ita kuwa Doi za ta yi gumurzu ne a wasan daf da na kuda da karshe ne da Timea Bacsinszky.