Dortmund ta dauki Ousmane Dembele

Image caption Dortmund ta dauki Ousmane Dembele a kwantaragin shekara biyar.

Borussia Dortmund ta dauki matashin dan wasa daga Rennes, Ousmane Dembele, kan yarjejeniyar shekara biyar.

Dan kwallon mai shekara 18, mai buga wa tawagar kwallon kafar Faransa ta matasa 'yan kasa da shekara 21, an alakanta cewar zai koma murza-leda a Tottenham ko Liverpool.

Dembele ya ci kwallaye 12 ya kuma taimaka aka zura biyar a raga, sannan shi ne matashin dan wasan da ya fi yin fice a Faransa a bana.

Borussia Dortmund tana mataki na biyu a kan teburin Bundesliga da maki 77, za kuma ta karbi bakuncin FC Koln a wasan karshe na gasar a ranar Asabar.