El-Kanemi ta ci Kano Pillars 2-0

Hakkin mallakar hoto Kano Pillars Twitter
Image caption Kano Pillars za ta karbi bakuncin Heartland va karshen mako.

El-Kanemi ta doke Kano Pillars da ci 2-0 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 16 da suka kara a Maiduguri ranar Alhamis.

Ibrahim Mustapha ne ya fara ci wa El-Kanemi kwallo a minti na 28 da fara wasa.

Bayan da aka dawo ne daga hutun rabin lokaci Hussaini Mustapha ya ci ta biyu.

Tun a ranar Laraba aka yi karawa takwas a gasar ta Firimiyar Nigeria wasannin mako na 16.

El-Kanemi Warriors za ta ziyarci Plateau United a wasan mako na 17 a ranar Lahadi.

Ita kuwa Kano Pillars za ta karbi bakuncin Heartland ne a karshen makon nan.