Za a tuhumi Kenya da karya ka'ida

Image caption Kenya za ta fuskanci takunkumi kan shan kwayoyi masu kara kuzari.

BBC ta fahimci cewar za a bayyana Kenya a matsayin kasar da ta karya dokar yin amfani da kwayoyi masu kara kuzari a wasa.

Idan kuma hakan ta tabbata wasu daga cikin fitattun 'yan wasan kasar ba za su sami damar shiga gasar wasannin Olympics da za a yi a bana ba.

Kenya wadda daya ce daga cikin kasashen da ta yi fice a wasannin tsalle-tsalle da guje-guje a duniya ba ta ciki wa'adin gwajin 'yan wasa kan shan kwayoyi masu kara kuzari.

Ana sa ran cewar hukumar kula da shan kwayoyi masu kara kuzari a wasa ta duniya za ta bayyana Kenya a matsayin wadda ba ta bin ka'ida.

Tun a baya hukumar ta gargadi Kenya da ta bi ka'idojin hukumar ko kuma a dauki matakin ladabtarwa a kanta.

A baya dai an yi zargi 'yan wasan Kenya da shan kwayoyi masu kara kuzari da kuma yin rufa-rufa sakamakon cin hanci da rashawa.