Pochettino zai kai har 2021 a Tottenham

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kociyan Tottenham, Pochettino da kociyan Leicester, Claudio Ranieri

Kociyan Tottenham, Mauricio Pochettino ya rattaba hannu kan kwantaragin tsawaita zamansa a kulob din har zuwa 2021.

An dai naɗa Pochettino mai shekara 44,a matsayin kociyan kungiyar, a watan Mayun 2014 domin horas da 'yan wasa na tsawon shekara biyar.

Pochettino, wanda dan kasar Argentina ne ya kai Tottenham matsayi na biyar a gasar Premier da kuma wasan karshe na gasar League Cup, a kakar wasa ta farko da ya yi a kulob din.

Tottenham din kuma za ta zama ɗaya daga cikin kungiyoyi ukun da ke sahun gaba a gasar Premier ta wannan kakar.

Pochettino ya ce " Mun yi imani cewa yanzu muka fara."