Za a yi wa Roberto Martinez bore

Hakkin mallakar hoto Getty

Magoya bayan Everton za su yi wa kocin kulob din, Roberto Martinez bore a daidai lokacin da yake shan matsin lamba domin ya sauka daga mukaminsa.

Kulob din dai shi ne na 12 a tebirin Gasar Premier ta Ingila, inda ya ci wasa daya kacal a cikin goma da ya buga.

Shugabannin kungiyoyin magoya bayan kungiyar sun sha alwashin yin bore a St. George's Hall da ke Liverpool, inda 'yan wasa da jami'an kulob din za su hadu domin cin abincin dare na karshe kakar wasa ta bana.

Frank de Boer, wanda bai dade da ajiye mukamin kociyan Ajax ba, ya ce yana son horas da Everton idan aka samu gurbin yin hakan.