Chelsea ta ƙara wa Terry shekara 1

Hakkin mallakar hoto
Image caption John Terry ya taimaka Chelsea ta dauki kofuna.

Kungiyar Chelsea ta karawa kyaftin din kulob din, John Terry kwantaragin shekara daya.

Sai dai kuma kulob din ya ce dan wasan yana duba yiwuwar karɓar kwantaragin.

Daman dai zaman Terry, mai shekara 35, zai ƙare ne a karshen kakar wasannin nan kuma an jiyo shi a watan Janairu yana cewa ba ya sha'awar tsawaita zamansa a kulob din.

A karshen kakar wasanni ne dai sabon kociyan kulob din, Antonio Conte zai fara horas da 'yan wasan Chelsea.