Arsenal ta ci kofin mata na FA

Image caption Arsenal ta ci kofin gasar FA ta mata a karon farko

Kungiyar kwallon kafar mata ta Arsenal ta samu nasarar lashe gasar kofin FA ta mata.

Kungiyar ta samu wannan nasara ce sakamakon cin kungiyar Chelsea da ta yi 1-0.

Danielle Carter ce ta jefa kwallo dayan da kungiyar ta ci cikin raga a minti daya na farko da fara wasan.

Ita ma 'yar wasan Arsenal Asisat Oshoala ta barar da damar cin kwallo har sau uku a lokacin wasan.

Arsenal ta samu wannan nasara ne a kan kungiyar Chelsea wadda take rike da kambun.