Zan cigaba da zama a Newcastle — Benitez

Hakkin mallakar hoto Getty

Rafael Benitez ya ce zai iya cigaba da zama a Newcastle a matsayin koci bayan tattaunawa mai ma'ana da ya yi da kulob din.

Benitez mai shekara 56 ya zama kocin kulob din ne bayan da aka kori Steve McClaren a watan Maris.

Kocin ya tabbatar da yiwuwar cigaba da zamansa a kulob din ne lokacin da aka tambaye shi kan hakan a wani taron manema labarai.

Ya ce, ''Za mu sake wasu tarukan. Abubuwan da muka tattauna duk masu ma'ana ne kuma za mu sake ganawa.''