Hull City ta doke Derby a zagayen farko

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hull City ta samu nasarar buga wasan karshe na gasar zakarun Turai sakamokon cin da tayi wa Derby County a zagaye na farko na wasan daf da na karshe.

Hull City ta ci Derby 3-0 ta hannun 'yan wasanta Abel Hernandez da Moses Odubajo da kuma Andy Robertson.

A ranar Talata ne za a yi zagaye na biyu na wasan a filin wasan KCOM Hull.

A ranar 28 ga watan Mayu ne kuma za a buga wasan karshe a Wembley.