An ci tarar Chelsea da kuma Tottenham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester ce ta lashe kofin Premier na bana kuma na farko tun kafa kungiyar shekara 132

An ci tarar Chelsea da Tottenham kudi kan kasa tsawatarwa 'yan wasansu a gasar Premier da suka kara.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta bukaci Chelsea da ta biya tarar kudi fam 375,000, ita kuwa Tottenham fam 225,000 za ta biya.

Kungiyoyin biyu sun fafata ne a gasar Premier wasan mako na 37 inda suka tashi 2-2 a Stamford Bridge.

A gumurzun an raba katin gargadi guda 12, kuma tarar da aka ci kungiyoyin biyu ta hada da yamutsin da suka yi a cikin fili da kuma bayan da aka tashi wasa.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta kuma ja kunnen kungiyoyin biyu da su guji sake aikata irin wannan laifin.