Leicester: Magoya baya na murnar ɗaukar kofi

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption 'Yan wasan Leicester suna murna.

Dubban magoya bayan kungiyar Leicester sun yi cincinrindo domin kallon faretin nuna murnar dangane da nasarar lashe kofin Premier Ingila da kulob ɗin ya yi.

Za a yi faretin ne a dandalin Jubilee Square da ke tsakiyar birnin na Leicester.

A ranar 7 ga Mayu ne dai aka ba wa Leicester kofin, a lokacin wasan da suka yi da Everton.

Leicester City ta kasance a ƙarƙashin teburin Premier, a kakar wasa ta bara.