West Ham za ta dauki Havard Nordtveit

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Havard Nordtveit tsohon dan kwallon Arsenal ne

West Ham United za ta dauko Havard Nordtveit daga Borussia Monchengladbach, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a bana.

Dan kwallon mai shekara 25, wanda ya bar Arsenal zuwa Jamus a Disambar 2010, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyar da Hammers.

A ranar 1 ga watan Yuni ne dan kwallon Norway mai wasan tsakiya zai koma West Ham, idan kwantiraginsa da kulob din na Jamus ta kare.

Nordtveit wanda ya fara buga wa tawagar Norway wasa a shekarar 2011, ya yi mata wasanni 28.