Renieri ne ya fi fice a gasar Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester ce ta lashe kofin Premier na bana kuma a karon farko

An bayyana kociyan Leicester City, Claudio Ranieri, a matsayin wanda ya fi yin fice a gasar Premier ta bana.

Kociyan mai shekara 64, ya lashe kyautar ne, bayan da ya jagoranci Leicester lashe gasar Premier a karon farko tun kafa kungiyar shekara 132 da suka gabata.

Renieri dan kasar Italiya shi ne koci na biyu da ya lashe kyautar wanda ba dan Biritaniya bane, bayan da Arsene Wenger na Arsenal ya karba a shekarar 2002 da kuma 2004.

Kocin ya lashe kyautuka guda uku sakamakon daukar kofin da Leicester ta yi, ciki har da wadda Italiya ta karrama shi a matsayin wanda ya fi fice a bana.

A gasar Championship kuwa kociyan Brighton, Chris Hughton, shi ne ya karbi kyautar.

A League One da kuma League Two Gary Caldwell, mai horar da Wigan shi ne kociyan da babu kamarsa.