An sa kyautar mota a damben gargajiya

Image caption Za a fara wasan gasar cin mota a ranar 20 ga watan Mayu

Kungiyar Marhaba da ke gudanar da wasan damben gargajiya a Minna, ta saka kyautar mota ga duk dan wasan da ya gagara a gasar da za ta saka.

Kungiyar ta tsayar da ranar 20 ga watan nan na Mayu, domin fitar da zakaran dambe da za ta ba shi motar hawa.

Shugaban kungiyar Shu'aibu Ado Yakasai ya ce sun yi shirin hakan ne da nufin zaburar da 'yan wasan damben gargajiya da kuma dawo da martabarsa ga masu sha'awar wasan.

Ya kuma ce a lokacin gasar za su gayyaci manyan 'yan wasa hudu daga Kudu da hudu daga Arewa da kuma guda hudu daga Guramada.

Bayan da kungiyar ta shirya bayar da mota ga wanda ya zama zakara a gasar, za kuma ta bai wa na biyu kyautar kudi naira dubu 100.

Za a yi wasannin ne a birnin Minna da ke jihar Niger a Nigeria.