An ɗagewa Fulham takunkumin sayen 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan kungiyar Fulham

Hukumar gasar League ta Ingila ta ɗagewa ƙungiyar Fulham takunkumin hana musayar 'yan wasa.

A watan Disamba ne dai aka ƙaƙabawa ƙungiyar ta Fulham takunkumin, sakamakon karya dokokin kashe kuɗaɗe.

Fulham ta yi asarar ƙuɗi fiye da ƙIma, a inda ta rasa £6m a kakar wasa ta 2014-15 sakamakon faɗowa daga gasar Premier Ingila.

Kociyan Fulham, Slavisa Jokanovic ya sayi 'yan wasa guda a watan Janairu, duk kuwa da cewa akwai takunkumin hana hakan.