Manchester United za ta buga gasar Europa

Image caption United za ta buga gasar Europa ta badi

Manchester United ta kammala a mataki na biyar a kan teburin Premier bana, bayan da ta ci Bournemouth 3-1.

United ta karbi bakuncin Bournemouth ne a kwantan wasan Premier da ya kamata su fafata a ranar Lahadi.

Rooney ne ya fara ci wa United kwallo saura mintuna biyu a je hutun rabin lokaci kuma ta 100 da ya ci a wasan Premier a filin wasa na Old Trafford.

Bayan da aka dawo ne daga hutun Rashford ya ci ta biyu, sannan kuma Young ya kara ta uku saura mintuna uku a tashi daga wasan.

Daf da za a tashi daga karawar ne dan wasan United Smalling ya ci gida, kuma hakan ya sa David de Gea ya kasa lashe kyautar golan da ya yi wasanni da yawa kwallo ba ta shiga ragarsa ba a Premier.

Yanzu haka mai tsaron ragar Arsenal Petr Cech shi ne ke kan gaba a matsayin wanda ya yi wasanni 16 kwallo ba ta shiga ragarsa ba a bana.

United ta kare a mataki na biyar a teburin ne da maki 63 za kuma ta shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa kai tsaye da za a yi a badi.

Tun da fari United ta bukaci cin kwallaye 19-0 domin ture Manchester City daga mataki na hudu a kan teburin Premier, domin buga gasar cin kofin zakarun Turai ta Champions League.