Heartland za ta kara da Plateau United

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Heartland ce ke mataki na daya a kan teburin gasar Firimiyar Nigeria

Plateau United za ta ziyarci Heartland a Owerri domin buga wasan mako na 18 a gasar Firimiyar Nigeria.

Heartland tana mataki na daya a kan teburin gasar da maki 31, yayin da Plateau United take matsayi na 14 da maki 21.

Wasu wasannin makon 18 da za a buga a gasar sun hada da karawa tsakanin Nasarawa United da Lobi Stars.

Wikki Tourist ta garin Bauchi za ta ziyarci Sunshine Stars ta Akure, sannan Shooting Stars za ta karbi bakuncin Abia Warriors.

Ranar Lahadi kuwa IfeanyiUbah da MFM za su yi gumurzu da kuma fafatawa tsakanin Niger Tornadoes da Kano Pillars.

Ga jadawalin wasannin :

Heartland FC Plateau United FC Ikorodu United FC Warri Wolves FC Sunshine Stars FC Wikki Tourists FC Shooting Stars FC Abia Warriors FC Rivers United FC Akwa United FC Nasarawa FC Lobi Stars FC Giwa FC Enyimba Int'l FC

Wasannin ranar Alhamis:

FC Ifeanyi Ubah MFM FC Niger Tornadoes FC Kano Pillars