Za a dakatar da wasu 'yan wasan motsa jiki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Brazil ce za ta karbi bakuncin wasannin Olympic da za a yi a bana

Sama da 'yan wasan motsa jiki 31 daga wasanni shida za a dakatar daga shiga gasar Olympics ta bana.

Shugaban kwamitin Olympics, Thomas Bach, ne ya sanar da wannan jawabin bayan da aka sake bincikar wasu 'yan wasa.

Kwamitin wasan na Olympic ya sake gwada 'yan wasa 454 daga cikin wadanda suka yi wasa a Beijin a 2008 kan fayyace idan sun sha kwayoyi masu kara kuzari.

Kwamitin ya ce ya sake yin gwajin ne da sabuwar na'ura da aka kirkiro, wadda babu irinta a fagen fasahar gwada 'yan wasa masu shan kwayoyi.

Haka kuma hukumar ta ce tana jiran sakamakon gwajin da ta yi wa 'yan wasa 250, wadanda suka fafata a gasar da aka yi a Landan a shekarar 2012.

Shugaban hukumar, Thomas Bach, ya ce suna sake yin gwaje-gwajen ne domin fitar da baragurbi daga wasannin tsalle-tsalle da guje-guje.