Rodgers da Mackay na son horar da Celtic

Image caption Celtic ce ta lashe kofin gasar kasar Scotland ta bana

Brendan Rodgers da Malky Mackay suna daga cikin masu horar da tamaula da suke zawarcin aiki a Celtic.

Celtic na neman kociyan da zai maye gurbin Ronny Deila, wanda ya ajiye aikin bayan da ya jagoranci kungiyar lashe kofin gasar bana.

Liverpool ce ta kori Rodgers mai shekara 43, daga aiki a cikin watan Octoban 2015.

Shi kuwa Mackay mai shekara 44, Wigan Athletic ce ta sallame shi daga jan ragamar kungiyar.

Wasu manyan masu horar da tamaula da suke son horar da Celtic sun hada da David Moyes da Roy Keane da Paul Lambert da Neil Lennon da kuma Steve Clarke.