Maza sun sha gaban Wayne Rooney — Shearer

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jamie Vardy, dan wasan Leicester ne kuma dan wasan Ingila, ya zarta Wayne Rooney.

Tsohon kyaftin na kungiyar wasa ta Ingila, Alan Shearer, ya ce yanzu haka ba Wayne Rooney ne ɗan wasan gaban da ya fi kowanne a ƙungiyar ba.

Sunan Rooney dai ya bayyana a jerin sunayen 'yan wasa 26 da za su buga gasar Euro ta 2016.

Shearer ya ce ɗan wasan, mai shekara 30, ya fi dacewa da zama ɗan wasan tsakiya, wato Harry Kane da Jamie Vardy sun yi masa zarra.

Alan Shearer ya ce "A koyaushe, kyaftin yana da rawar da zai taka, amma kuma batun cewa Rooney ne dan wasan gaba lamba ɗaya, ya kau."