Terry ya sabunta kwantaraginsa a Chelsea

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Terry ya yi nasarar daukar kofin Premier na Ingila hudu, da na FA guda biyar, da na League guda uku, da na Zakarun Turai da na Europa.

Dan wasan Chelsea John Terry ya sanya hannu a sabon kwantaragin shekara daya da kulob din.

A wani jawabi da ya yi mai sosa rai bayan wasan karshe da kulob din Chelsea ya yi da Leicester ranar Lahadi, dan wasan mai shekara 35, wanda kwantaraginsa ya kare a lokacin bazara, ya ce yana son ci gaba da murza leda a kulob din.

Terry ya ce, "Kowa ya san cewa ni dan wasan Chelsea ne gaba da baya. Ina sa ran murza leda a kakar wasa mai zuwa a karkashin sabon kociya, kuma ina fatan za mu kece raini."

Terry ya buga wa Chelsea wasa sau 703 tun lokacin da ya shiga kulob din a shekarar 1998.

Shugaban kulob din Bruce Buck ya ce: "Muna farin ciki John zai sake yin shekara daya a wannan kulob din".

Terry ya yi nasarar daukar kofin Premier na Ingila hudu, da na FA guda biyar, da na League guda uku, da na Zakarun Turai da na Europa.