An ci tarar Demichelis kan caca

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption An hana 'yan wasa da masu horar da tamaula yin cacar kwallon kafa

An ci tarar dan wasan Manchester City, Martin Demichelis, fan 22,058 bayan da ya karya ka'idar cacar kwallon kafa.

Dan wasan na tawagar Argentina ya yi cacar kwallon kafa sau 29 daga ranar 22 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Fabrairun shekarar nan.

A kakar wasan 2014/15 aka kafa dokar da ta hana 'yan wasa da masu horar da tamaula shiga wata sabga da ta shafi cacar wasanni.

Haka kuma an gargadi dan wasan da kada ya kara aikata laifin da ya yi.

Demichelis, mai shekara 35, ya koma City a watan Satumbar 2013 daga Atletico Madrid.