An sa ranar zaben shugaban UEFA

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shekara 16 Platini ya jagoranci hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai

Za a zabi sabon shugaban hukumar kwallon kafa ta Turai ranar 14 ga watan Satumbar shekarar nan.

Shugaban hukumar Michel Platini ne ya yi murabus daga kujerar da ya shugabanta tsawon shekara 16.

Ya kuma ajiye aikin ne a ranar 9 ga watan Mayu bayan da aka ki soke dakatarwar da aka yi masa daga shiga sabgogin tamaula.

An dakatar da Platini daga shiga harkokin kwallon kafa zuwa shekara shida, daga baya an rage su zuwa shekara hudu.

An samu Platini da laifin karya dokar da'ar ma'aikata, bayan da ya karbi ladan aiki sama da fam miliyan daya daga Fifa.

Wadanda za su yi takarar maye gurbin Platini sun hada da Michael van Praag da Aleksander Ceferin da kuma Maria Villar.

Duk wanda ya lashe zaben kujerar ta UEFA zai karasa wa'adin Platini da zai kare a Maris din 2019, zai kuma zama mataimakin shugaban Fifa.