Zan koma buga wasan tsakiya - Rooney

Image caption Rooney ya ci kwallo na 100 a gasar Premier a filin Old Trafford

Wayne Rooney na hangen makomar taka-ledarsa zuwa dan wasan tsakiya, bayan da ya taka rawa a karawa da Bournemouth.

Manchester United ce ta doke Bournemouth da ci 3-1 a kwantan gasar Premier da suka kara a Old Trafford ranar Talata.

Rooney ne ya ci kwallon farko kuma ta dari da ya ci a Old Trafford a gasar Premier, kuma shi ne ya taimaka aka ci ta uku a wasan.

Kociyan tawagar Ingila, Roy Hodgson ya fitar da 'yan wasa 27 na kwarya-kwarya da zai zabi wadanda za su wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai.

'yan wasan da ya zaba masu cin kwallo sun hada da Harry Kane da Jamie Vardy da Daniel Sturridge da Rooney da kuma Marcus Rashford.