Aston Villa zai dawo kan ganiyarsa

Image caption Aston Villa ya koma kurar baya a kakar wasannin ta bara.

Hamshaƙin attajirin nan ɗan kasar China da ya sayi kulob din kwallon ƙafa na Aston Villa ya ce yana da babban burin ganin kulob din ya ci gaba.

Shi dai Tony Xia yana so ne kulob din ya koma cikin gasar Premiya, kuma ya shiga sahun kulob shida da ke kan gaba.

An dai bayar da rahotannin cewar, attajirin ya sayi Aston Villa a kan kusan dalar Amurka miliyan casa'in.

Aston Villa ya koma kurar baya a kakar wasannin bara.