Bournemouth: Steve Cook zai kara shekara uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan, Bournmouth, Steve Cook a lokacin da ya kayar da dan wasan Leicester, Jamie Vardy

Dan wasan baya na Bournmouth, Steve Cook ya rattaba hannu a kan sabon kwantaragi na shekara uku, da kulob din.

Dan wasan mai shekara 25 dai ya je Bournmouth ne daga Brighton da Hove Albion, a 2011.

Cook ya buga wasanni 35 a kulob din, ya kuma zura musu kwallaye biyar.

Kociyan Bournmouth, Eddie Howe ya tabbatar da cewa kulob din ya yi watsi da tayin neman 'yan wasan kungiyar guda biyu, Matt Ritchie da Callum Wilson, a kan £20m da West Ham ta yi, ranar Talata.