English League: Tsarin kungiyoyi 100 a Ingila

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Yadda ake son kwallo a Ingila

Wata kila nan gaba a samu kungiyoyin wasa 100 domin fafatawa a gasa daban-daban ta wasannin kwallon kafa a Ingila.

Hukumar gasar League ta Ingila na son fito da wani sabon tsari wanda zai kunshi kungiyoyin wasa 20 a gasar wasanni daban-daban har guda biyar, daga kakar wasa ta 2019-20.

Hakan na nufin za a samu kungiyoyi 100 daga 92 da ake da su yanzu haka.

Yanzu haka dai akwai kungiyoyi 24 a gasar Championship da League One da League Two, a inda kuma gasar Premier League take da guda 20.

Hukumar ta gasar League ta ce sabon tsarin zai magance matsalar tsara lokacin wasa sannan kuma zai sa mambobin hukumar kara samun kudaden shiga.

Gasar Premier League da Hukumar FA sun amince da wannan sabon tsarin.

Sai dai kuma sauran kungiyoyi 72 na Championship da League One da League za su bayyana goyon bayansu ko akasin haka, a taronsu na karshen shekara, da za su yi a watan Yulin 2017.