Brendan Rodgers ya zama kociyan Celtic

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Brendan Rodgers ya zauna a Liverpool shekara uku

Kungiyar Celtic ta naɗa Brendan Rodgers a matsayin sabon kociyanta bisa kwantaragin wata 12.

Rodgers, mai shekara 43 wanda a baya ya horas da Liverpool da Swansea City da Reading da kuma Watford, zai maye gurbin Ronny Deila a Celtic.

Rodgers ya bar Anfield a watan Oktoba bayan kwashe shekara uku yana horas da 'yan wasan Liverpool din.

Brendan ya ce " zan yi iya bakin kokarina wajen dawo da magoya bayan kulob din tare da nishadantar da su da kuma yin nasara a wasanninmu."