Copa del Rey: Ran birnin Barcelona ya ɓaci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya bayan Barcelona

Magoya bayan Barcelona za su rike tutocin yankin Scotland guda dubu 10, a wasan karshe na gasar Copa del Rey wanda kungiyar za ta fafata da Sevilla, ranar Lahadi.

Hakan ya samo asali ne sakamakon aniyar gwamnati a Madrid ta kin amfani da tutar Kataloniya a lokacin wasan bisa abin da suka kira dalilan tsaro.

Yankin Scotland dai ya zabi da ya zauna a Birtaniya, a wata kuri'ar jin ra'ayin mutane da aka yi, a 2014.

Shi kuwa yankin Kataloniya bai samu wannan damar ba daga gwamnatin Spaniya.

Wani gungun masu rajin samawa yankin Cataloniya 'yanci, sun ce sun yanke shawarar yin amfani da tutocin na Scotland domin nunawa gwamnatin Spaniya irin abin da Kataloniyawan suke bukata.

A ranar Laraba ne dai Barcelona ta fitar da wata sanarwa kan hana amfani da tutar ta Katoliniyawa.