Moyes ya fice daga zawarcin Aston Villa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Moyes tsohon kociyan Everton da Manchester United

BBC ta fahimci cewar David Moyes ya bar neman aikin horar da kungiyar kwallon kafa ta Aston Villa.

Moyes mai shekara 53, yana daga cikin kociyoyi uku da ake sa ran daya zai maye gurbin Remi Garde.

Rabon da kociyan, dan kasar Scotland, ya jagoranci wata kungiya tun shekarar 2015, bayan da Real Sociedad ta sallame shi daga aiki.

Yanzu haka Nigel Pearson da Roberto Di Matteo ne suke neman aikin horar da Aston Villa din.

Ana tuninin cewar Moyes ya fice daga neman aikin horar da Villa ne saboda kungiyar za ta buga gasar Championship a badi.