Jarrabawa za ta hana Sobhi buga wasa

Hakkin mallakar hoto Getty

Ramadan Sobhi na Al-Ahly ba zai buga wasan cancantar gasar cin kofin kwallon Afirka ba a karawar da Masar za ta yi da Tanzania saboda zai rubuta jarrabawa.

Kungiyar Al-Ahly wanda ke bukatar maki guda kacal domin ta samu damar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a Gabon a shekarar 2017, za tu fafata da Tanzania a birnin Dar es Salaam ranar 4 ga watan Yuni.

Kocin Kulub din, Ihab Lehta ya sanar cewar, "Ramadan Sobhi ba zai iya murza leda ba a wasan gaba da za a yi saboda zai je Masar domin rubuta jarrabawar makarantar Sakandare.

Ya kara da cewar, "Za a yi wasan ranar 4 ga watan Yuni kuma a ranar 5 ga watan Yuni zai yi jarrabawar tasa, kuma ba za mu iya saya masa tikitin jirgi ba ta yadda da zarar an kammala wasan zai tafi.''

Sobhi ya taka wa kasar Masar muhimmiyar rawa a wasannin biyun karshe na wasan cancantar shiga gasar cin kofin Afirka na shekarar 2017.