Sullay Kaikai yana ruwan-ido

Hakkin mallakar hoto Getty

Sullay Kaikai na kungiyar Crystal Palace ya ce har yanzu bai yake shawara ba kan ko zai koma kasar Saliyo domin murza leda ko kuma ya ci gaba a Biritaniya.

Sullay, mai shekara 20, wanda iyayensa 'yan kasar Saliyo ne, an haifi shi a Birtaniya don haka yana da damar ya bugawa kasashen biyu wasa.

Dan wasan ya dage cewa yana bukatar ya kafa kansa a kungiyar Crystal Palace kafin ya fara murzawa kasarsa Saliyo leda.

Ya ce "Ba shawara ce da zan yanke ba a yanzu".

Sullay ya kara da cewa "Ina da sauran lokaci da zan iya yanke shawara kan kasar da zan murzawa leda.

Ya ce "A yanzu zan mayar da hankali kan kungiyar kwallon kafa ta. Akwai bukatar na dinga bugawa Crystal Palace kafin na yi tunanin murzawa kasata leda."

Kaikai ya fara gasar Premier ne a wasan karshe da Crystal Palace ta buga a kakar wasan da ta wuce inda Southampton ta doke su da ci 4-1.