Vardy ya kusa zama ango

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Vardy ya zura kwallo 24 a gasar Premier, lamarin da ya sa Leicester ta lashe kofin Premier.

Dan wasan gaba na Leicester City Jamie Vardy ba zai buga wasan sada zumucin da Ingila za ta yi da Australia ranar Juma'a ba saboda zai yi aure ranar Laraba.

A shekarar da ta gabata ne dan wasan, mai shekara 29, ya dage ranar daurin aurensa zuwa watan Yuni domin samun damar buga gasar Euro 2016.

Kocin Ingila Roy Hodgsonya ce Vardy "yana bukatar samun lokacin domin yin shagalin aurensa."

Vardy, wanda ya zura kwallon da ta bai wa Ingila nasara a kan Turkiyya da ci 2-1 ranar Lahadi ya ce: "Koci [Hodgson] ya bar ni na yi hutu ranar Laraba, amma zan dawo atisaye bayan ranar."

Vardy ya zura kwallo 24 a gasar Premier, lamarin da ya bai wa Leicester damar daukar kofin na Premier.