Kim Little ce gwarzuwar 'yar kwallon BBC

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kim Little ce ta biyu da ta lashe kyautar kwallon kafa ta mata ta BBC

'Yar kwallon Scotland Kim Little ce aka zaba a matsayin gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC ta bana.

'Yar wasan mai taka-leda a Seattle Reign ce ta lashe zaben da magoya baya suka yi, wanda hakan ya sa ta zama ta biyu da ta ci gasar.

Little ta yi nasara ne a kan wadanda suka yi takara da suka hada da Gaelle Enganamouit (FC Rosengard, Sweden), da Amandine Henry (Olympique Lyonnais), da Carli Lloyd (Houston Dash) da kuma Becky Sauerbrunn (FC Kansas City).

'Yar wasan mai shekara 25, ta ce ta yi mamaki da ta lashe kyautar, ta kuma yi farin ciki da aka karramata.

Little ta karbi kyautar a filin atisayen kungiyar da take yi wa tamaula a ranar Talata.