Liverpool ta dauki gola Karius

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool ba za ta buga gasar zakarun Turai ta bana ba

Liverpool ta sanar da daukar mai tsaron raga Loris Karius daga kungiyar Mainz, kan kudi fan miliyan 4.7.

Likitocin Liverpool sun kammala duba lafiyar Karius mai shekara 22, ya kuma sa hannu a kan yarjejeniyar shekara biyar, wadda za ta fara aiki ranar 1 ga watan Yuli.

Kwallaye da dama ya tare wa Mainz, wadda ta kammala kakar bana a mataki na shida a gasar Bundesliga daga wasanni 34 da ya tsare mata raga.

Dan kwallon wanda tsohon matashin dan wasan Manchester City ne zai yi gogayya da Simon Mignolet a sabon kulob dinsa.