An tafi hutu a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Za a shiga wasannin zagaye na biyu a gasar Firimiyar Nigeria

An bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa ta Nigeria, bayan da aka shiga zagaye na biyu a gasar kasar.

Hukumar gudanar da gasar ta Nigeria ta bayar da hutun mako biyu, domin kungiyoyin su shirya tunkarar wasannin zagaye na biyu.

Hakan na nufin an bude kasuwar sayen 'yan wasa a gasar ta Nigeria daga ranar Litinin 23 ga watan Mayu zuwa 3 ga watan Yuni.

Tun a ranar Juma'a aka fara buga wasannin mako na 19, inda aka kammala sauran fafatawar a ranar Lahadi 22 ga watan Mayu.