UEFA ta hukunta Man United da Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool ce ta fitar da Man United daga gasar Europa ta bana

An hukunta Manchester United da Liverpool, bayan da aka same su da laifin karya ka'idar kuwwar magoya baya a filin wasa.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai, UEFA, ce ta samu kungiyoyin biyu da laifi a karawar gasar cin kofin Europa da suka yi.

Hukumar ta ci tatar Manchester United kudi fan 44,342, yayin da Liverpool za ta biya fan 43,577, saboda jefa abubuwa cikin fili da tada yamutsi da magoya bayansu suka yi.

An kuma ci tarar Liverpool da kunna wuta mai tartsatsi da kin fara wasa a kan lokaci, yayin da United ita kuma ta yi laifin rufe matattakala a filin wasanta.

A hukuncin da aka yankewa Liverpool za kuma ta biya abubuwan da aka lalata a filin Old Trafford.

Tarar da aka yi wa kungiyoyin biyu ta hada da ta fan 15, 290, wadda aka dage har zuwa shekara biyu.