Shin ko kun san rana irin ta yau Liverpool ta ci UEFA ?

Hakkin mallakar hoto z
Image caption A bugun fenariti Liverpool ta ci Milan 3-2 a Santanbul

A rana irin ta 25 ga watan Mayu a shekarar 2005, Liverpool ta lashe kofin zakarun Turai a Santanbul babban birnin kasar Turkiya, bayan da ta ci AC Milan 3-2.

Tun kafin karawar, masana sun yi hangen cewar AC Milan ce za ta lashe kofin, wanda kafin nan ta lashe shi har sau shida ta kuma je wasan karshe a karo na 10 a lokacin.

Liverpool kuwa ta lashe shi ne sau hudu ta kuma kai wasan karshe a karo na shida a Santanbul.

Ana fara wasan Paolo Maldini ya ci wa Milan kwallo, Hernan Crespo kuma ya kara guda biyu kafin a je hutu--Milan 3 Liverpool babu.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Liverpool ta farke kwallayen ana saura minti shida a tashi daga fafatawar ta hannun Steven Gerrard da Vladimír Šmicer da kuma Xabi Alonso.

Hakan ya sa aka yi karin lokaci aka kuma tafi bugun fenariti, a nan ne Liverpool ta ci AC Milan 3-2.

Nasarar da Liverpool ta samu a karawar da ake yiwa taken abin mamaki a Santanbul ta sa ta dauki kofin gasar a karo na biyar, inda hukumar ta ba ta shi ya zama na dindindin.