Kwallaye 51 Ronaldo ya ci a bana

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid za ta buga wasan karshe a gasar zakarun Turai da Atletico Madrid ranar Asabar

Kwallaye 51 Cristiano Ronaldo ya ci a kakar wasan bana, a wasanni 48 da ya buga wa Real Madrid.

Da fara kakar wasannin shekarar nan Ronaldo ya fara cin kwallo a karawar da Espanyol ta sha kashi a hannun Madrid da ci 6-0, inda dan wasan ya ci biyar a karawar.

A gasar La Liga da Barcelona ta lashe kofin bana ya ci kwallaye 35, sai dai kuma Luis Suarez ne ya karbi kyautar wanda ya fi cin kwallaye a gasar, inda ya ci 40.

A gasar cin kofin zakarun Turai da Real za ta buga wasan karshe da Atletico Madrid a ranar Asabar, ya ci 16, kuma shi ne a kan gaba wajen cin kwallaye a gasar.

A dai kakar bana ya ci kwallaye uku (hat-trick) a wasa sau uku, ya kuma ci guda hudu sau biyu, yayin da ya ci kwallaye biyar a karawa daya sau daya.

Haka kuma Ronaldo bai karbi jan kati ba a wasannin bana, illa katin gargadi guda hudu da aka ba shi.