Kramaric ya koma wasa a Hoffenheim

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester ce ta lashe kofin Premier na bana a karon farko tun kafa kungiyar shekara 132

Dan kwallon da Leicester City ta saya mafi tsada a tarihin kungiyar Andrej Kramaric, ya koma Hoffenheim da murza-leda.

Kramaric dan kasar Croatia ya koma Leicester da murza-leda daga HNK Rijeka kan kudi fan miliyan 9.7 a cikin watan Janairun 2015.

Sai dai kuma wasanni bakwai ya buga wa Leicester City a kakar bana, daga nan ne ta bayar da shi aro ga Hoffenheim a cikin watan Janairu.

Dan kwallon ya ci wa Hoffenheim kwallaye biyar a wasanni 15 da ya buga mata tamaula.

Hoffenheim za ta ci gaba da buga gasar Bundesliga ta Jamus a badi.