An ci kwallaye 359 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto npfl Twitter
Image caption Za a shiga zagaye na biyu a gasar ta Firimiyar Nigeria

An zura kwallaye 359 a raga a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka yi wasanni 167.

Tuni aka tafi hutun zagaye na biyu a gasar, an kuma bude kasuwar sayen 'yan kwallo daga ranar 23 ga watan Mayu zuwa 3 ga watan Yuni.

Cikin kwallayen da aka ci, guda 93 kungiyoyin da suka buga wasanninsu a waje ne suka ci su.

Kungiyoyin da suka fi cin kwallaye a gasar sun hada da Enugu Rangers wadda ta ci 26, sai Kano Pillars mai kwallaye 25 a raga, yayin da Sunshine Stars ta ci 23.

Wikki Tourist ce ke kan gaba a matsayin wadda aka ci karancin kwallaye, inda 11 suka shiga ragarta.

Enyimba ce a matki na biyu wadda aka ci kwallaye 12, Warri Wolves da kwallaye 13 suka shiga ragarta.